14 Yuli 2021 - 11:27
Mutane Kimanin 45 Suka Mutu A Rikicin Afirka Ta Kudu

Rahotanni daga Afirka ta Kudu, na cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon tarzomar data barke bayan kama tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, sun kai 45.

ABNA24 : Bayanai sun ce an samu mutum 26 da suka rasa rayukansu a yankin Kwazulu-Natal, inda nan ne aka fara samun rikicin ranar Juma’a, sai kuma wasu 19 a wajajen Johannesburg, kamar yadda alkalumman da hukumomin yankunan suka fitar.

ko a wannan Talatar, an fuskanci kone-kone da kuma wawashe dukiyoyin jama’a duk da kiraye kirayen da hukumomin kasar sukayi na a kwantar da hankali, da kuma jibge sojoji.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana tarzomar da ta barke a yankunan biyo bayan kama Jacob Zuma a matsayin mafi muni da aka taba gani tun bayan kawo karshen mulkin wariya a kasar.

342/